3 Agusta 2016 - 09:51
Boko Haram Sun Kai Hari A Janar Difa

Kungiyar Boko Haram ta sake kai wani mumunan hari a yankin Bosso na Jihar Diffa dake kudu maso gabashin Jumhoriyar Nijer

A tsakanin ranar Lahadi 31 ga watan Yulin da ya gabata zuwa ranar Litinin 1 ga watan Augusta, Mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kai wani mumunan harin ta'addanci  a kauyukan Bosso dake jihar Diffa na kudu maso gabashin kasar, inda suka yiwa fararen hula sama da 50 yankan rago.

An kai harin ne a gabashin garin Gaduraa na Karamar hukumar Bosso dake kusa da iyakar kasar da Tchadi, harin ya rutsa da kabilun Pulani buduma, Mohamid da kuma kuburis kuma mafi yawan mutanan da harin ya ritsa da su 'yan kabilar Buduma ne.

Sama da shekara guda kenan da kungiyar Boko Haram din ta fara kai hare-haren ta a Jumhoriyar Nijer, inda alkaluma ke cewa daga wancan lokacin zuwa yanzu mayakan boko haram din sun kashe jami'an tsaro gami da fararen hula da dama a kasar.288